Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Harin Da Boko Haram Ta Kai Wa Dakarun Najeriya


Sojojin Operation Lafiya Dole sun ceto wata tsohuwa da jikarta daga wani sansanin 'yan Boko Haram.

Rahotanni sun ce maharan sun kwashi makamai da albarusai a harin da suka kai akan Bataliya ta 157 da ke Metele, a karamar hukumar Abadam a jihar ta Borno da ke arewa maso gabashin Najeriya.

Mayakan Boko Haram sun kai hari akan bataliyar dakarun Najeriya a jihar Borno.

Rahotanni sun ce, harin ya yi sanadin mutuwar kwamandan dakarun bataliyar, sannan an sojoji da dama sun mutu.

Wasu rahotannin sun ce adadin wadanda suka mutu ya haura 50.

Jaridar Premium Times ta yanar gizo ta ruwaito cewa maharan sun kwashi makamai da albarusai a harin da suka kai akan Bataliya ta 157 da ke Metele, a karamar hukumar Abadam a jihar ta Borno.

Rahotanni sun ce harin ya auku ne da misalin karfe 6 na yamma a ranar Lahadi, ya kuma zo ne yayin da dakarun na Najeriya ke kokarin kada mayakan na Boko Haram zuwa kuryar arewa maso gabashin yankin na jihar ta Borno.

A ‘yan kwanakin nan, mayakan na Boko Haram sun zafafa hare-haren da suke kai wa a yankin jihar ta Maiduguri, lamarin da ke kara jefa fargaba a zukatan mutanen yankin.

A baya, dakarun Najeriya sun yi ta ikrarin samun nasara akan mayakan na Boko Haram.

Facebook Forum

Shin PI Za Ta Fashe Kuwa Ko Yaudara Ce Kawai?

Karin bayani akan Bidiyo
XS
SM
MD
LG