WASHINGTON D.C. —
Ministan makamashi a Saudiyya, ya ce hare-haren jirage mara matuka da mayakan Houthi suka kai akan matatun man fetur din kasar na Aramco guda biyu, sun yi sanadiyyar rage adadin man da kasar ke fitarwa.
Wani hoton bidiyo da wani da ba kwararre ba ne ya dauka, ya nuna yadda wuta take ci, amma zuwa tsakiyar rana an ga hayaki ya turnuke sararin samaniya.
Hukumomin Saudiyya sun ce babu wanda ya rasa ransa ko ya ji rauni daga hare-haren.
Tuni dai kakakin mayakan Houthi, Kanar Yahya Saree, ya tabbatar da cewa su suka kai hare-haren, yana mai cewa za su ci gaba da kai iri-irensu idan dakarun da Saudiyya ke jagoranta suka ci gaba da kai masu hari.
Za ku iya son wannan ma
-
Afrilu 30, 2022
An Ware 20-30 a Matsayin Satin Rigakafi Na Duniya
-
Afrilu 24, 2022
Kudin Kujerar Zuwa Hajji Zai Karu Zuwa Naira Miliyan 2.5