Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Harin Kano Ya Hallaka Mutane 8 Kuma An Kama Wani Mai Hannu a Ciki


Kano School Of Hygiene Bomb Blast
Kano School Of Hygiene Bomb Blast

Kakakin rundunar 'yan sandan jahar Kano A.S.P Magaji Musa Majiya ya tabbatar da haka a tattaunawar su da Bello Habeeb Galadanchi.

Kakakin rundunar 'yan sandan jahar Kano A.S.P Magaji Musa Majiya ya tabbatar da harin da aka kai makarantar koyon aikin kiwon lafiya a kan titin jami'ar Bayero da ke Kano. Kuma ya ce daga cikin mutane ishirin da aka kai asibiti, takwas sun riga mu gidan gaskiya:
please wait

No media source currently available

0:00 0:02:54 0:00
Shiga Kai Tsaye

Kafin Kakakin rundunar 'yan sandan jahar Kanon ya yiwa Bello Habeeb Galadanchi bayani, wakilin Sashen Hausa a Kano Muhammad Salisu Rabiu ya bayar da bayanan farko-farko inda ya ce wani dalibi ya shaida mi shi cewa a wajen ajiye motoci aka boye bom din da ya tashi:
please wait

No media source currently available

0:00 0:02:02 0:00
Shiga Kai Tsaye

Bayan wannan bayani na wakilin Sashen Hausa Muhammad Salisu Rabiu, shi ma Anas Saminu Ja'en wani shaida dake tsaye a bakin makarantar ya ganewa idon shi yadda aka fitar da wadanda harin ya rutsa da su, ya ce da idon shi ya ga an fitar da kimanin mutane goma jina-jina.
please wait

No media source currently available

0:00 0:01:01 0:00
Shiga Kai Tsaye

Kakakin rundunar 'yan sandan jahar Kani A.S.P Magaji Musa Majiya ya ce bayan an kwashe wadanda harin ya rutsa da su, masanan kwance boma-bomai sun kara duba ko'ina ko da wani bom a makale a wurin, amma ba su gani ba. A.S.P Magaji Musa Majiya an kama wani mutumin da aka ga alamun rashin gaskiya tare da shi, wanda kuma tuni aka tuhuma da hannu a cikin kai harin. Kuma Ya kara da cewa kwamishinan 'yan sandan jahar Kano ya sa a zafafa sintiri a makarantun Kano, kuma su na ci gaba da daukan matakai daban-daban, da na fili, da na boye domin kare rayukan jama'ar jahar Kano.
XS
SM
MD
LG