Accessibility links

Harin Kunar Bakin Wake A Birnin Mogadishu

  • Ibrahim Garba

Tarkacen wasu daga cikin motocin da harin birnin Mogadishu ya rutsa da su.

Hukumomi a Somalia sun ce wani dan kunar bakin wake da mota, ya kai hari kan wata tawagar motoci a birnin Mogadishu

Hukumomi a Somalia sun ce wani dan kunar bakin wake da mota, ya kai hari kan wata tawagar motoci a birnin Mogadishu da ke rakiyar wasu wakilai daga kasar Qatar, ya hallaka ‘yan Somaliya 8.

‘Yan sanda sun ce ‘yan Qatar din dai ba su ko raunana ba, kuma sun karasa zuwa otal dinsu.

Nan take dai babu wanda ya dau alhakin kai harin na yau Lahadi, to amman mayakan al-Shabab na da tarihin tayar da hankali a wurin.

Al-Shabab ta yi iko da akasarin birnin Mogadishu har sai lokacin da sojoji su ka fattake mayakan daga babban birnin kasar shekaru biyu da su ka gabata.
XS
SM
MD
LG