Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Harin Kunar Bakin Wake Ya Hallaka Mutane 17 Tare da Raunata Wasu 50 A Iraqi


Wurin da aka kai kunar bakin wake a Bagadaza babban birnin Iqaki

‘Yan kunar bakin wake sun hallaka mutane 17 kana sun jima wasu 50 rauni a yankin’yan shi’a dake gundumar Bagadaza babban birnin Iraqi, kamar yadda rundunar ‘yan sanda da jamiaan kiwon lafiya suka ruwaito.

A kalla mutane 8 ne suka mutu nan take kana wasu 29 suka samu rauni lokacin da wani dan kunar bakin wake ya tayar da bomb din da yayi jigida dashi a sabuwar birnin Jadidi Bagdad dake zamewa babban birnin kasuwancin kasar.

Haka kuma wani dan kunar bakin waken ya tada nashi a babban titin da ake hada-hadar kasuwanci na Bayaa dake kudancin birnin na Bagadaza inda shi kuma yayi dalilin mutuwar mutane a kalla tara kana wasu 22 suka ji rauni kamar yadda majiyar ke cewa.

A shafin yanar gizo da yan taaddan suka saba anfani dashi, wani da ya bayyana kansa a matsayin dan kungiyar IS ya bayyana kansa a matsayin wanda yake da alhaki kai wannan harin, yana cewa yayi niyyar auna ‘yan kungiyar Shia’a ne.

Wadannan yan kungiyar Sunni sun sha kai hare-hare boma-bomai ga ‘yan shi’an Iraqi wadandfa suke ganin suna da alaka da gwamnartin kasar ta Iraqi.

XS
SM
MD
LG