Accessibility links

Harin Kunar Bakin Wake Ya Kashe Mutane Akalla 14 A Damaturu.

  • Aliyu Imam

'Yan kato da gora suka kafa shingaye a Maidguri.

Al'amarin ya auku ne a kofar shiga kasuwar lokacinda ake kokarin tantance yarinyar.

Wasu nakiyoyi da wata 'yar kunar bakin wake ta tayar a wata kasuwa a jihar Yobe dake arewa maso gabashin Najeriya, sun kashe akalla mutane 14.

Shaidun gani da ido suka ce akalla mutane 50 ne suka jikkata.

Jami'ai a jihar suka ce fashewar ta auku ne da safiyar lahadin nan a kofa shigar kasuwar dake Damaturu babban binrin jihar Yobe.

Babu wanda ya fito ya dauki alhakin kai harin. A farkon wannan wata akalla mutane 9 ne suka halaka lokacinda wata 'yar harin kunar bakin wake ta auna masu masu sallar idi.

Ga karin bayani.

Ahalinda ake ciki kuma wani bam da aka boye cikin wata mota ya tashi a harabar wani O'tel a Mugadishu a ranar lahadin nan, ya kashe akalla mutane 13.

A cikin O'tel din ne kuma ofisoshin jakadancin kasashen China da Masar suke.
Kungiyar mayakan sakai ta al-shabab ta dauki alhakin kai wannan hari.

XS
SM
MD
LG