Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Harin Kunar Bakin Wake Ya Kashe Mutane Takwas a Unguwar Jakadun Kasashen Waje a Kabul, Afghanistan


Wurin da aka kai harin kunar bakin wake a Kabul

Kungiyar ISIS ta dauki alhakin harin kunar bakin waken da aka kai a unguwar jakadun kasashen waje a Kabul babban birnin kasar Afghanistan, harin ya yi sanadiyar mutuwar mutane takwas kuma an aunashi ne kan yankin dake kusa da ofishin jakadancin Amurka

Wani dan kunar bakin wake ya kai hari a unguwar da ke mazaunin ma’aikatun jakadancin kasashe a Kabul, babban Birnin Afghanistan, inda ya kashe mutane takwas, sannan ya raunata wasu da dama, a cewar wasu jami’an ma’aikatar lafiyar kasar.

Tuni dai kungiyar IS ta dauki alhakin wannan hari.

Bam din ya kaikaici wani yanki ne mai makeken shingen tsaro da ke kusa da ofishin jakadancin Amurka, a daidai lokacin da ake tsaurara matakan tsaro a yankin, sanadiyar hare-haren da ake yawan kai wa a ‘yan makwannin nan.

A farkon watan Oktoba, wani dan kunar baki wake ya tada da bam a cikin wata mota shake da ababan fashewa a kusa da wata makarantar horar da dakarun Afghanistan a babban Birnin na Kabul, harin da ya yi sanadin mutuwar kurata 15 sannan ya raunata wasu da dama.

Kungiyar Taliban ta dauki alhakin kai wannan hari.

A kusan wannan lokacin ne kuma, wani maharin dauke da bam ya kutsa kai cikin wani masallaci da ke makare da Musulmi ‘yan Shi’a ya kashe masu ibada 50 a Birnin na Kabul, harin da shima kungiyar IS ta ce ita ta kitsa shi.

Facebook Forum

Shin PI Za Ta Fashe Kuwa Ko Yaudara Ce Kawai?

Karin bayani akan Bidiyo
XS
SM
MD
LG