Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Harin Pakistan Ya Halaka Mutane 20


Wani wuri da aka kai harn bam a Pakistan

Jami’an kasar Pakistan sun ce yau Juma’a wani hari kunar bakin wake na wani bam mai karfi ya ratsa wani Masallaci dake cunkushe da mutane a arewa maso yammacin Pakistan.

Rahotanni sun ce harin ya yi sanadin mutuwar akalla mutane 23 ya kuma raunata wasu 30.

Wani mai magana da bangaren haramtattaciyar kungiyar Taliban da ya balle mai suna Jama'atul Ahrar ya ce kungiyar sa ce ke da alhakin kai harin.

A lokacin da ta tuntunbi Muryar Amirka, kungiyar ta ce harin ya auna Masallacin ne saboda wakilan wata kungiyar 'yan yakin sa kai dake goyon bayan gwamnatin kasar da ake kira Peace Committee suna cikin masu ibada a Masallacin.

XS
SM
MD
LG