Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Harry Kane Na Nan Daram A Tottenham – Nuno Espirito Santo


Dan was Ingila/Tottenham, Harry Kane

Akwai rahotanni da ke cewa, abokanan wasan Kane sun ce mai yi wa dan wasan ba zai koma kungiyar ta Tottenham a kakar wasa mai zuwa, saboda ana alakanta shi da tafiya kungiyar Man City.

Sabon kocin kungiyar kwallon kafa ta Tottenham a Ingila, Nuno Espirito Santo, ya ce ba ya tantama, dan wasan kungiyar Harry Kane zai ci gaba da zama a kungiyar a kakar wasa mai kamawa.

“Ba ni da haufi. Fatana ga Harry shi ne, ya smau lafiya ya kuma huta da kyau.” Santo ya fada a wani taron manema labarai kamar yadda Sky Sports ya ruwaito.

“Harry dan wasanmu ne, fakat. Babu hurumin a rika wata Magana. Yanzu lokaci ne da zai huta. Idan ya dawo za mu tattauna. Na zaku ya dawo cikin kungiyar.”

Dangane da dan was anta Gareth Bale, Nuno ya tabbatar da cewa, dan wasan na Real Madrid ba zai dawo kungiyar a kakar wasa mai zuwa ba.

Akwai rahotanni da ke cewa, abokanan wasan Kane sun ce mai yiwa dan wasan ba zai koma kungiyar ba, saboda ana alakanta shi da tafiya kungiyar Man City.

Dubi ra’ayoyi

UEFA Euro 2020: Italiya

Karin bayani akan Wasanni
Ba Laifi Ba Ne Don Na Dawo Kano Pillars – Ahmed Musa
please wait

No media source currently available

0:00 0:00:59 0:00
Karin bayani akan Diego Maradona
XS
SM
MD
LG