Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Haruffan sadarwa ta internet OMG! sun shiga kamus na Oxford


Kamus na turanci

Kamus na turanci mai suna Oxford ya kara wadansu gajejjerun kalamai da aka fi amfani da su a hanyar sadarwar internet a sabon Karin da yayi.

Kamus na turanci mai suna Oxford ya kara wadansu gajejjerun kalamai da aka fi amfani da su a hanyar sadarwar internet a sabon Karin da yayi. A wani yunkuri irinshi na farko kuma, kamus din zai sa alamar zuciya wanda ya kasance sabon abu, a matsayin fi’ili da yake nuna kauna. Kamus din zai kuma kunshi gajejjerun kalamai ko kuma haruffan da ake amfani da su kamar “OMG” da ke nufin Oh My God, watau ‘wayyo Allah na” da kuma “LOL” da ke nufin “Laught Out Loud” watau a bushe da dariya” Kamus na Oxford dai shine kamus mafi sahihanci da yafi kowanne Kamus din turanci bayanan kalamai a duniya. Daga cikin sababbin kalaman da aka kara a kamus din akwai “moffin top” dake nufin guru ko kibar kugu, da kuma kalma “wag” dake nufi mata da ‘yan mata. Sai kuma “Banh mi” wanda yake nufin hadin burodin kasar Vietnam. Ana kara sababbin kalamai da kuma bayanai ne a kamus din kowanne wata uku,

XS
SM
MD
LG