Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Yau Jumma'a Alkali A Afirka Ta Kudu Zai Yanke Hukumci Kan Takardar Neman Belin Henry Okah


Tsohon madugun MEND, Henryn Okah, lokacin da ake fitowa da shi daga cikin kotu Alhamis 14 Oktoba, 2010 a birnin Johannesburg.
Tsohon madugun MEND, Henryn Okah, lokacin da ake fitowa da shi daga cikin kotu Alhamis 14 Oktoba, 2010 a birnin Johannesburg.

Masu gabatar da kara a Afirka ta Kudu sun ce tsohon madugun kungiyar MEND shi ne ya kitsa munanan hare-haren na Abuja

Masu gabatar da kararraki na Afirka ta Kudu sun ce wani tsohon 'yan tsagera na Najeriya yana da hulda da wadanda suka shirya munanan hare-haren bam da suka hallaka mutane a Abuja, babban birnin Najeriya.

An kama Henry Okah, tsohon madugun kungiyar MEND, a inda yake zaune a birnin Johannesburg, jim kadan a bayan hare-haren da suka kashe mutane 12.

Henry Okah a lokacin da aka fito da shi daga cikin kotu a Johannesburg, Alhamis 14 Oktoba, 2010.
Henry Okah a lokacin da aka fito da shi daga cikin kotu a Johannesburg, Alhamis 14 Oktoba, 2010.

A lokacin da aka yi zama jiya alhamis domin nazarin bukatar da ya gabatar ta neman a ba da belinsa, masu gabatar da kararraki sun ce Okah shi en kanwa uwar gami wajen kitsa harin na bam, suka kuma ce 'yan sanda sun gano rasidai na sayen bindigogi da rokokin harba gurneti.

Okah ya musanta cewa yana da hannu a hare-haren, yana mai fadin cewa 'yan siyasar Najeriya masu neman cimma wani gurinsu na siyasa su ne suke neman shafa masa kashin kaji.

Kotun ta Johannesburg ta dage zama kafin ta yanke shawara kan ko zata ba da belin nasa. Za a ci gaba da zama a yau jumma'a.

Ana zargin Okah da hannu a tagwayen hare-haren bam da aka dasa cikin motoci biyu, wadanda suka kashe mutane 12 a lokacin bukukuwan cikar shekaru 50 da samun 'yancin kan Najeriya a farkon watan nan.

Hukumomin Najeriya sun kama wasu mutanen su tara dangane da hare-haren.

XS
SM
MD
LG