Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

'Yan Bindiga Sun Kama wata Shugabar makaranta Mallakar Kamfanin Mai Exxon Mobil A Yankin Nija Delta


Hotn henry Okah daya daga cikin shugabannin mayakan sakai na MEND a yankin Niger Delta

Rahotanni daga Najeriya sunce wasu 'yan bindiga sun kama shugabar wata makaranta, mallakar kamfanin mai Exxon Mobil a garin Eket,cikin jihar Akwa Ibom.

Rahottani daga Nigeria sunce wasu ‘yan bindiga sun sace wata macce shugabar wata makaranta ta kampanin man fetur na Exxon Mobil, har ma sun kashe direbanta da dansanda dake gadinta.

Wani jami’in ‘yansanda yace a garin Eket na jihar Akwa Ibom dake yankin Niger Delta ne wannan al’amarin ya wakkana. Ita maccen, wacce Ba’indiya ce da ake kira Lakshmi Tombush, an ce itace shugabar makarantar Pegasus. Har zuwa yanzu dai hukumomi basu bada wata alamar dake nuna an nemi a biya diyya a kanta ba, amma dai ‘yansanda na ci gaba a binciken lamarin.

Ta wani bangaren kuma…hukumomin na Nigeria sun tabattarda cewa wasu mutane dake dauke da bindigogi kuma suna tafe akan Babura, sun harbe wani dansanda dake gadin gidan wani babbar kusar gwamnati a arewancin Nigeria. A garin Bauchi ne wannan al’amarin ya faru jiya da dare, garin da a cikinsa ne kwanan baya ‘yan Boko Haram suka fasa gidan kurkuku, suka saki fursunoni sunfi 700.

Har yanzu hukumomi suna binciken harbin na jiya, kuma izuwa yanzu basu riga suka dora laifin harbin akan ‘yan kungiyar ta Boko Haram ba. A yanzu hakan ma ma’aikatan tsaro na can suna ta sintiri a kan titunan garin Maidugurin jihar Borno inda ake dora laifin tash-etashen hankulla, harda kashe-kashe akan su ‘yan Boko Haram din.

XS
SM
MD
LG