Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

An Yiwa Gwamnan Neja Ca Bayan Ya Soki 'Yan Maulan Jihar


A makon da ya gabata ne gwamnan Neja ya ayyana wasu manyan biranen jihar a matsayin inda aka fi samun karancin abinci da kuma jama'a 'yan maula.

An sami biyo bayan cece-kuce sakamakon kalaman da gwamnan jihar Neja a Najeriya Alhaji Abubakar Sani Bello yayi, akan cewa an fi samu ‘yan maula da karancin abinci a wasu manyan biranen jihar.

Yayi wannan jawabin ne a wani taron jama’a inda yace, “idan ka ga ana yunwa a manyan birane ne irin su Minna da Bidda da Kontagora, wuraren da yawancin mutane ba sa son yin aiki ko sana’ar yi.

Wadannan kalaman ba su yiwa mutanen jihar da dama dadi ba, ciki har da wasu ‘yan mahaifarsa ta Kontagora. Malam Shehu Musa Tanko Kontagora yace, batun maular nan bai yi masu dadi ba, kuma mutanen garinsu na sana'ar noma. Ya kara da cewa bai kamata Shugaba yayi irin wadannan kalaman ba.

Gwamna Abubakar sani Bello ya yiwa Muryar Amurka karin haske akan abinda yake nufi da cewa, abin da yake fata shine ya ga kowa ya sami abin yi, kowa ya iya kula da iyalinsa.

Ya kara da cewa mutanen Kontagora ne suka fi tada jijiyar wuya akan wannan batun. Amma bayanin da yayi a cewarsa ya so ne iyaye su sa ido akan ‘ya'yansu musamman ma matasa, saboda akwai wadanda aka samarwa ayyukan soja amma suka watsar.

A halin da ake ciki, gwamnan yace, suna dab da bude wasu makarantun koyor da sana’o’in hannu a sassan jihar Neja da za su taimaka wajen rage yawan matasan da basu da aikin yi, wanda rashin aikin na haifar da maula a cikin al'umma.

Ga karin bayani cikin sauti a rahoton Wakilinmu na Jihar Neja.

please wait

No media source currently available

0:00 0:03:05 0:00

Facebook Forum

XS
SM
MD
LG