Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Hillary Clinton Ta Kalubalanci Rasha Kan Batun Syria


'Yan Syria su na kallon wani tankin sojojin gwamnati da 'yan tawaye suka ragargaza a garin Ariha dake wajen Idlib a arewacin Syria a ranar lahadi 10 Yuni 2012

Yayin da babban jami'in ayyukan kiyaye zaman lafiya na Majalisar Dinkin Duniya yace yanzu kasar ta shiga cikin yakin basasa gadan-gadan.

Sakatariyar Harkokin Wajen Amurka Hillary Clinton ta ce Amurka ta damu da rahotannin da ke nuna cewa Rasha na kai jirage masu saukar ungulu na yaki zuwa Syria, a sa’ilinda babban jami'in ayyukan tabbatar da zaman lafiya na Majalisar Dinkin Duniya kuma ke cewa, a yanzu kam wannan kasar ta Larabawa ta fada yakin basasa gadan-gadan.

Sakatariya Clinton ta fadi a yayin wata tattaunawa a cibiyar nazarin manufofi ta Brookings a nan birnin Washington cewa ikirarin Rasha cewa batun kai makamanta kasar Syria bai da nasaba da tashin hankalin da ke faruwa ba gaskiya ba ne ko misqala zarratin. Ta ce Amurka ta tinkari Rasha da bukatar ta dakatar da cigaba da kai kayan yaki zuwa kasar Syria, wadda tashin hankali na tsawon watanni 15 ya daidaita.

Wadannan kalaman na ta sun zo ne a daidai lokacin da babban jami'in ayyukan tabbatar da zaman lafiya na Majalisar Dinkin Duniya, Herve Ladsous, ya gaya wa ‘yan jarida cewa kasar ta Syria na fuskantar karuwar tashe-tashen hankula sosai kuma a yanzu ta fada yakin basasa sosai.

Ya ce dakarun tawaye sun kwace wurare da dama kuma gwamnati na son ta sake kwato su ta wajen amfani da tankokin yaki da atilare da kuma jiragen yaki masu saukar ungulu.

XS
SM
MD
LG