Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Hillary Clinton Ta Kusa Zama Yar Takarar Shugaban Kasa Ta Jam'iyyar Democrat


Hillary Clinton, 'yan jam'iyyar Democrats
Hillary Clinton, 'yan jam'iyyar Democrats

A siyasarAmurka kuma,tsohuwar sakatariyar harkokin wajen Amurka Hillary Clinton jiya Talata ta kara matsawa kusa da zama mutuniyar da zata zamma 'yar takarar shugabancin Amurka ta jam'iyyar Democrat.

Bayan da aka kammala kidaya kusan duka kuri'u da aka kada a zaben fidda gwani a jihar Kentucky, Clinton doke Bernie Sanders.

Sakamakon zaben bashi da wani tasiri domin a jam'iyyar Democrat, 'yan takarar suna raba wakilan gwargwadon yawan kuri'u da dan takara ya samu ne, saboda haka a zaben na Kentucky, da alamun yan takarar zasu raba wakilai 61 daga jihar.

A wani zaben fidda gwani da aka yi a jhar Oregon jiya Talatan, rahotanni suna nini d a cewa Senata Bernie Sanders ne zai lashe jihar.

Senata Sanders zai bukaci ya lashe kashi 85 cikin dari na sauran zabubbuka da suka rage idan har zai wuce Madam Clinton, lamarin da yake da matukar wuya domin tana bukatar wakilai kasa da dari daya ne yanzu yayinda da Sanders ke bukatan wakilai fiye da dari bakwai.

Jam'iyyar Democrat tana da zabubbuka a tsibirin Virgin, da kuma yankin Puerto Rico ranakun 4 da 5 na watan Yuni, amma wakilai da za'a samu a can, basu kai ta sami wakilan da ake bukata domin ta zama 'yar takara ba. Ana jin zata sami nasarar yin hakan a zabukan da za'a yi ranar 7 ga watan Yuni, lokacinda jihohi shida zasu yi zaben fidda gwani.

Bernie Sanders
Bernie Sanders

XS
SM
MD
LG