Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Shin Ko Amurkawa Zasu Zabi Shugaba Ko Shugabar Kasa Mai Nutsuwa?


Trump Clinton Commander in Chief Forum

‘Yar takarar shugabancin Amurka ta jam’iyar Democrat Hillary Clinton tace, abu mafi muhimmanci ga kowane shugaban kasa shine ya kasance mai natsuwa. Yayinda abokin hamayyarta na jam’iyar Republican Donald Trump yace, kada irin halinsa da tunaninsa su dami masu kada kuri'a.

Clinton ta bayyana haka ne jiya Laraba a wani shirin tashar Telebijin ta NBC mai suna "Dandalin Babban Kwamanda" ko kuma “Commander in Chief Forum” a turance, da aka gudanar a birnin NY. Shirin dai tamkar soman tabin muhawara uku da ‘yan takarar zasu yi ne. Clinton da Trump dukansu sun amsa tambayoyi kan harkokin tsaro.

Sun amince cewa, ba zasu yi amfani da wannan dandalin wajen caccakar juna ba, sai dai loto loto suka rika cakunar juna.

Clinton tace, shugaban kasa yana bukatar kasancewa mutum da yake sauraron mutane, ya yi nazari kan abinda aka gaya mashi ko mata, tace natsuwa da kuma sanin ya kamata, suna da muhimmanci.

Ta bayyana amfani da karfin soji a matsayin mataki na karshe, tace yakin Iraq darasi ne. Tace ita ma tayi kuskure wajen goyon bayan yakin lokacin da take ‘yar majalisar Dattawa. Clinton tace, Amurka ba zata sake tura sojan kasa suyi yaki a Iraq ba.

Clinton tace, tilas ne Amurka ta nemi Karin goyon bayan abokan kawancenta na kasashen larabawa a yaki da IS.

A nasa gefen, Trump ya shaidawa dandalin cewa, zai yi matukar taka tsantsan yayinda yake tunanin tura sojojin Amurka bakin daga, ya kuma zargi Clinton da cewa "ita macce ce mai son yin anfani da makaman yaki matuka."

Yace ya yi mamakin wadansu bayanan sirri kan tsaron kasa da ake yiwa manyan ‘yan takarar shugaban kasa, sai dai ba zai bayyana ko menene ya bashi mamaki ba.

Clinton da Trump zasu yi muhawararsu ta farko ranar ishirin da shida ga watan Satumba. Zata kasance muhawara ta farko cikin jerin muhawarori uku da za a yi kafin ranar takwas ga watan Nuwamba, ranar da za a zabi wanda zai gaji shugaba Barack Obama.

XS
SM
MD
LG