Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Hillary Clinton Ta Yiwa Donald Trump Fatan Alheri


Hillary Clinton yayinda take jawabin amincewa da shan kaye a zaben shugabancin kasar
Hillary Clinton yayinda take jawabin amincewa da shan kaye a zaben shugabancin kasar

Yar takarar shugabancin kasar Amurka a karkashin lemar jami’iyar Democrats Hillary Cliunton ta bayyana amincewarta da sakamakon zaben da aka kamalla a ranar Talatar shekaranjiya inda ta taya wanda aka zaba din Donald Trump na Republican, kuma ta yi mishi fatar samun nasara a jagorancin da zai yiwa Amurkawa.

Sai dai Clinton tsohuwar sakatariyar harkokin wajen Amurka da tayi zumudin zama mace ta farko shugaban Amurka, ta nuna matukar bakin cikinta ga rashin samun nasarar a wannan zabe. Ta fadi hakan ne a birnin New York a lokacin da da take jawabi ga magoya bayanta, tana cewa wannan abu nada ciwo kuma zai dauki lokaci mai tsawo ana juyayi a kansa.

Clinton ta gargadi magoya bayan nata cewar su ci gaba da yakin neman abin da ya zama hakkinsu.

Shugaban Amurka Barrack Obama, wanda ya taka muhimmiyar rawa wurin yiwa Clinton yakin neman zabe, ya fada a fadar White House cewa zai bada cikakken hadin kai a don samar da ingantaccen jagorancin kasar a karkashin sabon shugaban da aka zaba, Donald Trump.

Obama yace duk da irin cece-kuccen da ya faru a yakin neman zabe na tsawon lokaci wanda kuma ya kara zurfafa raba kawuna a siyasar Amurka, karshenta za’;a fahimci cewa su duka dai Amurkawa ne masu kishin kasarsu.

Ya kuma gayyaci Donald Trump zuwa fadarsa ta White House yau Alhamis don su tattauna a kan shirye shiryen mika mulki da za ayi a ranar 20 ga watan Janairun sabuwar shekara mai zuwa.

Trump hamshakin dan kasuwa mai hada hadar gine gine kuma mai kalamai masu jan hankali, shine ya fara zama shugaban Amurka na farko da ba’a taba zabensa ba a wani ofishin gwamnati kuma bai taba aikin soja ba ko rike wani babban mukamin gwamnati ba.

Trump mai shekaru 70 da haifuwa, shine shugaban Amurka na farko mafi yawan shekaru da zai jagoranci kasar na wa’adin shekaru hudu.

XS
SM
MD
LG