Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Hizbulla na ci gaba da sa rai akan Iran


Hoton Shugaban Hizbullah Hassan Nasrullah

‘Yan kungiyar shi’ar kasar Lebanon na Hezbollah sun ce, har yanzu zasu ci gaba da sa rai da taimakon da suke samu daga kasar Iran duk da ‘yarjejeniyar Nukiliyar kasar da manyan kasashen duniya masu fada a ji.

Shugabansu Hassan Nasrullah ne ya bayyanawa magoya bayansu haka a jiya Asabar. Yace alakarsu da Iran ta akida ce wacce itace kan gaba fiye da ta huldar diflomasiyyar duniya.

Iran dai itace babbar mai tallafawa Hezbollah da makamai, wanda kuma kungiya ce da Amurka ta sa a jerin kungiyoyin ‘yan ta’adda a duniya. Musamman ma yadda suke kira ga darkake kasar Isra’ila daga doron kasa da yiwa kasashen yammacin Turai barazana.

A yanzu haka dai akwai mayakan Hezbollah dake fadan marawa sojojin Bashar Al-Assad baya. Amurka tace taimakon Iran ga Hezbollah da ‘yan Houthis abin damuwa ne.

XS
SM
MD
LG