Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Hon Sabi: Ba Maganar Ibrahim Magu Sai Dai Fadar Shugaban Kasa Ta Bada Wani


Majalisar wakilan Najeriya, ta ce tana nan a kan matsayinta, na kin amincewa da Ibrahim Magu, ya zama shugaban hukumar masu bata dukiyar kasa ta Najeriya, (EFCC).

Shugaban kwamitin labarai na majalisar dattawan Sanata Aliyu Sabi Abdullahi, ya ce batun Ibrahim Magu, babu shi, sai dai fadar shugaban kasar ta sake tura masu wani mutum na daban kamar yadda ya bayyana a hirarsu da wakilin sashen Hausa na muryar Amurka, Mustapha Nasiru Batsari.

Da yake Magana akan shugaban hukumar Kwastam, Kanal Hamid Ali, mai ritaya, Sanata Sabi Abdullahi, ya ce majalisar dattawan ta yanke matsayinta na tilas yayi murabus.

Dan majalisar dattawan ya yi wannan bayani ne a lokacin bude wani taron bita da aka shirya ma wasu malaman Firamare, a garin Kontagora dake jihar Neja, da nufin kyautata harkokin koyarwa a yankin.

Malaman Firamaren guda dari da ashirin 120, ne aka shiryawa wannan horaswa ta musamman da Sanata Sabi Abdullahi, ya ce ya kashe sama da kudi Naira Miliyan Goma sha Biyar domin basu horon.

Daga Minna, Mustapha Nasiru Batsari ya aiko mana da wannan rahoton.

please wait

No media source currently available

0:00 0:02:58 0:00

Facebook Forum

Shugaba Joe Biden ya zama Shugaban Amurka na 46

Fashin baki kan rantsarda da shugaba Joseph Biden da Kamala Harris

BIDIYO: Fashin baki kan rantsarda da shugaba Joseph Biden da Kamala Harris
please wait

No media source currently available

0:00 0:06:51 0:00

An rantsar da sabon shugaban Amurka Joe Biden da mataimakiyarsa Kamala Harris

BIDIYO: An rantsar da sabon shugaban Amurka Joe Biden da mataimakiyarsa Kamala Harris
please wait

No media source currently available

0:00 0:02:35 0:00

Bikin Rantsar da Joseph R. Biden a Matsayin Shugaban Amurka na 46

Bikin Rantsar da Joseph R. Biden a Matsayin Shugaban Amurka na 46
please wait

No media source currently available

0:00 1:45:22 0:00
XS
SM
MD
LG