Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Hong Kong Ta Dakatar Da Shirin Mika Masu Laifi Ga China


Shugabar yankin Hong Kong Carrie Lam, yayin wani taron manema labarai a yau Asabar 15 ga watan Yuni 2019

Ita dai wannan doka da yankin na Hong Kong yake so ya kirkiro, ta kunshi aikawa da duk wani da ake zargi da aikata wani babban laifi zuwa China domin a yi masa shari’a.

Hukumomin yankin Hong Kong, sun dakatar da wani shiri na mika wadanda ake tuhuma da manyan laifuka ga kasar China domin a yi musu shari’a, shirin da ke kunshe a wani kuduri wanda ya haifar da gagarumar zanga zanga.

A yau Asabar shugabar yankin ta Hong Kong, Carrie Lam, ta bayyana cewa, za a dakatar da shirin har sai sun kammala tuntubar masu ruwa da tsaki kan lamarin

“Bayan tuntuba da aka yi ta cikin gida cikin kwanaki biyun da suka gabata, ina mai sanar da ku cewa, gwamnati ta yanke shawarar dakatar da yin sauyi ga dokar, sannan za mu fara tattaunawa da dukkan bangarorin da abin ya shafa," a cewar Lam.

Ita dai wannan doka da yankin na Hong Kong yake so ya kirkiro, ta kunshi aikawa da duk wani da ake zargi da aikata wani babban laifi zuwa China domin a yi masa shari’a.

Wannan shiri ya fargar da al’umar yankin na Hong Kong, wadanda suka ki amincewa, lura da irin banbanci dokoki da bangarorin biyu ke da su.

Wannan shiri ya kuma sha suka daga kasashen waje, inda Amurka ma ta yi Allah wadai da shi.

Facebook Forum

XS
SM
MD
LG