Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Hukumar Alhazan Najeriya Ta Sake Sabon Tsarin Ciyar Da Alhazai.


Alhazai sun taru kusa da birnin Makka mai tsari a Saudiya ranar Litinin 14 ga watan Oktoba shekarar 2013.

An bullo da tsarin ciyar da alhazan Najeria, sabanin yadda ake barin Alhaji ya nemi abinci da kansa.

Yanzu ana iya cewa jigilar Alhazan Najeriya an sha karfin sa domin yanzu makonni 4 kenan da fara wannan aiki.

Abinda ya dauki hankalin a wannan shekarar shine irin tsarin ciyar da Alhazai da hukumar Alhazan ta Najeriya tayi, wajen tabbatar da kyawon abinci da za a baiwa Alhazan, sabanin irin tsarin da ake yi ada.

A shekarun da suka gabata akan baiwa Alhaji kudin abincin sa a hannun sa ne, kana ya nemi abinda zaici da kansa, amma wannan karon abin yasha ban-ban.

Musali Hajiya Hussaina Abba Yarima ta zo aikin Haji ne daga jihar Nassarawa, kuma ta shaidawa wakiliyar sashen Hausa Madina Dauda cewa.

‘’Shekaru 36 da suka gabata lokacin data yi aikin Hajjin ta na farko, su Alhazai sune suke ciyar da kansu, da dai sauran bukatun su, amma wannan karon da suka zo cinsu da shansu duka a Hotel din da suke zaune ne ke daukar dawainiyar hakan, bayan wurin kwanan su’’.

Ga Dai Madina Dauda da Karin Bayani.

please wait

No media source currently available

0:00 0:03:06 0:00

Facebook Forum

Laftanar Janar Farouk Yahaya

Makasan Sheikh Goni Aisami Sun Bata Sunan Sojin Najeriya – Laftanar Janar Farouk Yahaya
please wait

No media source currently available

0:00 0:02:11 0:00
Karin bayani akan Bidiyo

Shin da gaske NNPP ba ta yi wa Shekarau adalci ba?

Karin bayani akan Bidiyo
XS
SM
MD
LG