Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Hukumar Kula Da Wasannin Motsa Jiki Na Olympics Ta Zabi Paris A Matsayin Inda Za Ayi Wasannin Shekarar 2024


Rio Olympics Athletics
Rio Olympics Athletics

An zabi kasar Paris domin ta dauki dawainiyar shirya wasannin shekarar 2024.Hukumar kula da wasannin motsa jiki ta duiniya ce tabada wannan sanarwan, yayin da tace a shekarar 2028 ko Los Angeles nan Amurka ne za a gudanar da wannan gasar.

Hukumar shirya wassanin motsa jiki na Olympics (IOC) ta bada sanarwar cewa birnin Paris na Faransa ne ta zaba ya dauki dawainiyar shirya wassanin shekarar 2024 yayinda shi kuma birnin Los Angles na nan Amurka aka bashi wassanin 2028.

A jiya ne Hukumar ta IOC ta bada wannan sanarwar a hedkwatarta dake Peru.

Wassanin 2024 da birnin Paris zai gudanar zasu zama karo na farko a cikin shekaru 100 da birnin ya dauki nauyin su tun bayan wassanin Olympics din ya gudanar a shekarar 1924, kuma zai zama karo na ukku da birnin na Paris ya dauki nauyin wasannain. Ya fara gudanar da su ne a shekarar 1900.

Shima birnin Los Angeles wadanan wassanin na 2028 sune zasu zama karo na ukku da ya taba daukar nauyin wassanin Olympics bayanda ya gudanarda na shekarun 1932 da 1984.

Wannan na nufin rabon Amurka baki dayanta da daukar bakuncin wadanan wassanin yau shearu 32 cif ke nan.

Facebook Forum

XS
SM
MD
LG