Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Hukumar Alhazan Najeriya Sai Ta Tantance 'Yan Najeriya da Suka Rasu Zata Bar Saudiya -


Shugaba Muhammad Buhari

Bisa ga umurnin da shugaban Najeriya Muhammad Buhari ya bayar, sai hukumar alhazan Najeriya ta tantance duk 'yan Najeriya da suka rasu a turmutsitsin Saudiya kana zata bar kasa mai tsarki.

Hukumar Alhazan Najeriya ta kara tabbatar da karin alhazan da suka rasa rayukansu a hanyar tafiya jifar Shedan da ya haura adadin mutane 199 kamar yadda ta bayyana a alkaluman baya.

To saidai cikin mutanen akwai wasu 'yan Najeriya mazauna Saudiya da babu ciakkakun bayanai akansu da su ma suka rasa rayukansu.

Shugaban hukumar alhazan Barrister Abdullahi Mukhtar Muhammad da ya je yin bankwana da rukunin alhazai na karshe ya ce zai zauna da sauran manyan jami'an hukumar a Saudiya saboda tantance duk alhazan da suka rasu.

Yace bisa ga umurnin shugaban kasa zasu cigaba da zama a Sadiya har sai sun kama tantance 'yan kasar da suka rasa rayukansu. Yace cikin wadanda suka rasa rayukansu za'a samu suna na dan Najeriya ne amma ba lallai ya je aikin hajji ba ne. Ya na iya zama mazaunin kasar ko kuma dalibi ne ko kuma je aikin umura amma bai koma gida ba. Suna kokarin su kiyaye domin kada su bada bayanin da ba haka yake ba.

Hukumar ta koyi wani daratsi daga wata hajiya 'yar jihar Kwara.wanda ya sa daga badi hukumar zata rabawa alhzai layin salula da za'a dinga aika masu sakon gaggawa.

Ga karin bayani.

please wait

No media source currently available

0:00 0:02:58 0:00
Shiga Kai Tsaye

Laftanar Janar Farouk Yahaya

Makasan Sheikh Goni Aisami Sun Bata Sunan Sojin Najeriya – Laftanar Janar Farouk Yahaya
please wait

No media source currently available

0:00 0:02:11 0:00
Karin bayani akan Bidiyo

Shin da gaske NNPP ba ta yi wa Shekarau adalci ba?

Karin bayani akan Bidiyo
XS
SM
MD
LG