Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Hukumar Alhazan Najeriya Ta Shirya Bitar Fadakar da Maniyata Akan Cutar Ebola


Alhazai a birnin Mkka.

Hukumar alhazan Najeriya ta shirya bitar fadakar da kawunan maniyata akan cutar ebola inda cibiyar yaki da cututtuka ta Amurka ta bayyana taimakawa Najeriya da magunguna da jami'ai.

Jami'ar cibiyar yaki da cututtuka ta Amurka dake Najeriya wadda ta halarci taron bita da hukumar alhzan Najeriya ta shirya akan fadakar da alhzai, tace da Amurka ta ji bullar ebola a Najeriya ta taimaka da jami'ai da kayan aiki.

Cibiyar ta kuma taimaka ta hanyar bada magunguna da bin sawun cutar da tara bayanai domin dakile yaduwarta.Mrs Catherine ta cibiyar a Najeriya tace Amurka zata cigaba da taimakawa domin a hana cutar bazuwa.

Shi ma wakilin jakadan Saudiya a Najeriya ya ba 'yan Najeriya kwarin gwiwa yana fatan a samu waraka akan irin wadannan cututtukan zamani.

A likitance dai an dauki duka matakan dakatar da cutar a Legas da yiwa maniyatan albishirin zasu shiga Saudia da yadda Allah inji mataimakin ministan kiwon lafiya na Najeria Dr. Haliru Alhassan. Yace yana fatan an kawo karshen cutar. Ba zata wuce Legas ba balantana ta ketara zuwa arewa.

Hukumar kiwon lafiya da cibiyar cututtuka ta Amurka duk sun yaba da matakan da Najeriya ta dauka na ganin cutar bata yadu ba.Dr Haliru yace zasu cigaba da kara himma domin duniya ta gani kuma ya bukaci 'yan jarida su ma su taimaka wajen watsa labarai suna kiran jama'a su kwantar da hankalinsu su kuma kara tsafta. Wanke hannu nada mahimmanci domin yana taimakawa wajen rage yadar cututtuka.

Sani Bala Kalarawi ya bukaci al'ummar musulmi su kara da addu'a. Yace ruwan Zanzam, Annabi ya tabbata cewa duk wanda ya shashi da niyar samun waraka Allah zai warkar dashi. Idan musulmi na aikin ibadarsa ta kullum babu yadda za'a sameshi da kazanta.

Maniyatan Najeriya zasu samu shiga Saudiya amma sai dai za'a samu karin tsanani wajen tantancewa.

Ga rahoton Nasiru Adamu El-Hikaya

please wait

No media source currently available

0:00 0:02:21 0:00
Shiga Kai Tsaye

Dalilin Da Ya Sa Nake Sana’ar Sayar Da Shayi Duk Da Cewa Ni Kansila Ne

Dalilin Da Ya Sa Nake Sana’ar Sayar Da Shayi Duk Da Cewa Ni Kansila Ne - Dayyabu Lawal Bala
please wait

No media source currently available

0:00 0:03:52 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA

Bikin Lasar Gishiri

Yadda Aka Yi Bikin Lasar Gishiri A Jamhuriyar Nijar
please wait

No media source currently available

0:00 0:03:32 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA
XS
SM
MD
LG