Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Hukumar Alhazan Nigeria ta bada sanarwar kudin hajjin bana

Makka (file photo)

Hukumar Alhazan Nigeria ta bada sanarwar kudin aikin hajjin bana mai matakai uku, dababa da matsakaciya da kuma karama. Farashin ya karu da kimamin kashi takwas daga cikin dari idan aka kwatanta da abinda manyaci ya biya a bara.

Baban Kujera dubu dari shidda ne da ashirin da daya da dari hudu da casa’in da tara da kwabo saba’in da biyar, karama kuma za’a biya akalla za’a biyar naira dubu dari biyar da ashirin da maitan da arba’in da tara da kwabo saba’in da biyar.

Uba Mana jami’in labaru na hukumar alhazan ya baiyana cewa dalilai guda biyu ne, ya kawo karin farashin. Na farko kudin gidaje a Macca ya karu, sa’anan kuma kudin mai na jirgin sama yayi tashin gwaron zabi. Idan dai Allah ya kaimu, ya kuma yarda, a ranar biyar ga watan oktoba za’a fara jigilar Alhazai zuwa kasa mai tsarki

XS
SM
MD
LG