Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Human Rights Watch Ta Yi Kaca-Kaca Da Hukumar EFCC


Tmbarin Kungiyar Human Rights Watch
Tmbarin Kungiyar Human Rights Watch

Kungiyar ta ce EFCC ta zama ta jeka-na-yi-ka, saboda tabarbarewar shugabanci da cuwa-cuwar cikinta da kuma katsalandar din siyasa da ake mata

Wata kungiyar rajin kare hakkin dan adam ta ce hukumar yaki da cin hanci da rashawar Nijeriya, EFCC, ba ta yi wani abin a-zo-a-gani ba wajen hana manyan ‘yan siyasa sata.

A wani rahoton da ta gabatar yau Alhamis, kungiyar Human Rights Watch ta ce Hukumar Yaki Da Ta’annati da dukiyar jama’a EFCC, ta zama ta jeka-na-yi-ka, saboda tabarbarewar shugabanci da cuwa-cuwar cikinta da kuma katsalandar din siyasa da ake mata.

Kungiyar da ke a nan Amurka, ta soki hukumar EFCC saboda zartas da hukunci kan manyan ‘yan Nijeriya hudu kawai tunda aka kafa ta a 2003.

Rahoton ya kuma yi nuni da zarge-zargen sama da fadi da rashin iya shugabancin da ake wa shugabar hukumar ta yanzu, Farida Waziri.

Kungiyar ta Human Rights Watch ta yi kira ga gwamnatin Nijeriya, da ta zage damtse a yakinta da cin hanci da rashawa.

Shugaba Goodluck Jonathan ya sha alwashin kawar da cin hanci da rashawa, wanda wannan wata babbar matsala ce cikin gwamnatin Nijeriya da kuma ‘yan siyasa tun shekara da shekaru.

Kungiyar Yaki da cin hanci da rashawar nan ta Transparency International, ta sha bayyana cewa Nijeriya na daya daga cikin kasashen da aka fi cin hanci da rashawa cikinsu a duniya.

XS
SM
MD
LG