Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Hukumar CIA: Haspel Ta Ce Ba Ta Goyon Bayan Tsarin Azabtarwa


Gina Haspel, wadda ake tantancewa domin ta zama shugabar CIA kuma macce ta farko da za ta rike mukamin

Yayin da da majalisar dattawan Amurka ke tantance Gina Haspel, matar da za ta maye gurbin Mike Pompeo a hukumalekena asiri ta CIA, ta yi alkawarin gujewa azabtar da wadanda ake tuhuma domin tatsar bayanai.

Matar da shugaban Amurka Donald Trump ya zabo ta shugabanci hukumar leken asirin kasar ta CIA, ta yi wa yan majalisa alkawarin cewa ba za ta dawo da tsarin nan na tsananta neman bayanai daga hanun fursunoni ba, ta hanyar azabtar da su.

Idan har aka tabbatar mata da mukamin Haspel za ta zama mace ta fakro da za ta shugabanci hukumar.

Mai shekaru 61, Haspel ta kwashe kimanin shekaru 30 a wannan hukumar tattara bayanan sirri a matsayi daban-daban, amma tana aikin nata ne a bayan fage.

Facebook Forum

Shin PI Za Ta Fashe Kuwa Ko Yaudara Ce Kawai?

Karin bayani akan Bidiyo
XS
SM
MD
LG