Hukumar cin hanci da rashawa ta kasar Indonesia ta kama kakkakin majalisan dokokin kasar, kan zargin da yana da hanu a balakalar satar kudi dala Amurka miliyan dari da saba'in.
A jiya Lahadi ne aka kama aka tsare Setya Novanto, a wata cibiyar ta tsare mutane, mai magana da yawun hukumar cin hanci da rashawa ya ce za 'a tsare shi na tswon kwanaki 20 domin a yi masa tambayoyi.
Ya karyata duk wani zargi da ake yi masa.
Hukumomi sun zargi Novanto da kasancewa cikin rukunin jami'an da suka yi amfani da wata sabuwar tsarin yin katin shida na yan kasa domin satan kudaden gwamnati.
Yan sanda sun yi kokarin kama Novanto a satin da ya gabata amma ba a same shi a gida ba.
Facebook Forum