Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Hukumar dake Yaki da Cin Hanci da Rashawa A Nijar Ta Bankado Malaman Bogi


Salissou Oubandoma, mataimakin shugaban hukumar dake yaki da cin hanci da rashawa ko HALICIA a Nijar
Salissou Oubandoma, mataimakin shugaban hukumar dake yaki da cin hanci da rashawa ko HALICIA a Nijar

Kimanin miliyan dubu biyu na kudin sefa ne gwamnatin Nijar ke hasara a duk shekara wajen biyan malaman kwantiragi na bogi akalla a jihohi biyar kawai da yanzu aka kammala bincike

Mataimakin shugaban hukumar Salissou Oubandoma yace a bincikensu sai su tarar mutum guda an sa sunasa a wurare biyu ko ukku.

A cewarsa jihohi biyar kawai suka kammala , kenan yawan kudin da kasar ke hasara akan malaman bogi kawai ka iya haurawa sama fiye da sefa miliyan dubu biyu. Yanzu saura jihohi ukku da hukumar zata bincika.

Wani abun da suka gano kuma shi ne a aji guda ana iya iske malai bakwai. Yayinda malami guda yana bada karatu sauran suna waje. Yace ko a sakandare ma za'a sami malami yana koyaswa ne kawai na awa biyar. Sauran lokacin kuma ya je yayi abun da ya ga dama amma kuma ana biyansa cikakken albashi.

Sai dai Munkaila Halidu shugaban kungiyar malaman kwantiragi yace allura ce take shirin tono garma. Yace laifin ba na malaman kwantiragi ba ne amma laifin wadanda suka daukan malaman kuma suke biyansu. Su ne suke dauka su ne kuma suke biya, ke nan su ne suke cuwa cuwa. Yace daga kasa har zuwa sama sun san abun dake faruwa.

Ga rahoton Souley Barma da karin bayani.

please wait

No media source currently available

0:00 0:03:22 0:00

Hawan Nasarawa, jihar Kano a Najeriya, lokacin da aka gudanar da bukukuwan Sallar Eid el Fitr
please wait

No media source currently available

0:00 0:03:44 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA
XS
SM
MD
LG