Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Hukumar FBI Ta Ce Laifuka da Suka Jibanci Kin Jini ko Kyama Na Karuwa a Amurka


 Daraktan Hukumar FBI, Christopher Wray
Daraktan Hukumar FBI, Christopher Wray

Hukumar dake binciken manyan laifuka a Amurka ta ce shekaru biyu a jere laifuka da suke da alaka da kin jinin Musulmai da Spaniyawa da masu canza jinsinsu sai karuwa su keyi a kasar Amurka

Shekaru biyu kenan a jere aikatata laifuffukan da suka danganci nuna kin jinni ko kyama suka mamaye Amurka, inda hare-haren da aka auna kan Musulmai da Spaniyawa da kuma mutanen da suka sauya halittar su ke ci gaba da karuwa, a cewar hukumar binciken manyan laifuka ta Amurka FBI.

Kididdigar hukumar FBI ta wannan shekarar da aka fitar jiya Litinin kan laifukan da ake aikatawa saboda kyamar jinsi ko addini ko halittar mutum, ta nuna cewa a shekarar 2016 an samu ire-iren wannan laifuka har 6,121 wanda hakan ke nuna cewa an samu karuwar laifukan da kashi 4.6 daga cikin 100 daga laifuka 5,850 da aka aikata a bara.

Facebook Forum

XS
SM
MD
LG