Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Hukumar HALCIA Da Sufeton Bincike Sun Gana Kan Yaki Da Cin Hanci


HALCIA - Nijar
HALCIA - Nijar

Shugabannin hukumar yaki da cin hanci a jamhuriyar Nijar sun gana da sufetocin dake da alhakin gudanar da bincike a ma’aikatatun gwamnati da nufin tantauna hanyoyin hada karfi domin tunkarar matsalar cinhanci da rubda ciki akan dukiyar jama’a da ta yi kamari a kasar.

Ganin yadda wasu matsaloli ke dabaibaye aikin sufetocin gwamnati a yayin gudanar da bincike a ofisoshin ministocn gwamnatin kasar ta Nijar ya sa hukumar HALCIA kiran wani taron da ya hada jami’anta da wadannan sufetoci domin tattauna hanyoyin da za a bullo wa wannan matsala dake maida hannu agogo baya wajen yakar cin hanci da kuma farautar mahandama dukiyar jama’a. Alhaji Sallissou Oubandoma shine matemakin shugaban hukumar HALCIA.

A ci da karfafa wannan sabon mataki shugabannin hukumar sun fara hangen kafa cibiyar zuba ido da bin diddigin ayyukan bincike a kowane ofisoshin ministan gwamnatin wannan kasa.

Sufetocin sun yaba da wannan yunkuri domin a cewarsu mataki ne da zai basu damar gudanar da aiki cikin nutsuwa ba tare da wani katsalandan ba kamar yadda sufeton kasa Gounabi Adamou ya bayyana.

A watan jiya hukumar yaki da cin hanci ta bada sanarwar bankado sama da million 2000 na cfa wadanda suka makalle a hannun wasu kamfanoni da masana’antun gwamnati da masu zaman kansu wadanda suka hada da kudaden haraji da wadanda aka yi ruf da ciki a kansu.

Hukumar ta HALCIA ta lashi takobin lekawa duk inda ya dace domin karbo kudaden da aka wawure a matsayinta na mai kare dukiyar kasa daga barayin biro da abokan cuwa cuwarsu.

Saurare cikakken rahoton Sule Barma a Sauti:

please wait

No media source currently available

0:00 0:03:05 0:00

Hawan Nasarawa, jihar Kano a Najeriya, lokacin da aka gudanar da bukukuwan Sallar Eid el Fitr
please wait

No media source currently available

0:00 0:03:44 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA
XS
SM
MD
LG