Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Hukumar Kiwon Lafiya Ta Duniya Ta Ce Shayar Da Nonon Uwa Shi Zai Ceci Rayukan Jarirai


Shayar Da Nonon Uwa

Yayin da aka shiga makon karfafa shayar da nonon uwa, hukumar ta WHO ta ce nonon uwa ne kadai ke da sinadaran da zasu iya kare lafiyar jarirai da yara kanana

Hukumar Kiwon Lafiya ta Duniya, WHO, ta ce shayar da nonon uwa yana da matukar muhimmanci ga ceto rayukan yara. A wannan mako da aka shiga na karfafa shayar da nonon uwa a duniya, hukumar ta WHO da sauran cibiyoyin kiown lafiya su na jaddada matakai goma na tabbatar da nasarar shayar da nonon uwa.

Hukumar Kiwon Lafiyar ta Duniya ta bayyana nonon uwa a zaman abincin da ya fi dacewa ga jarirai da yara kanana. Ta ce nonon uwa ba ya da illa, kuma yana ba jarirai irin sinadaran da suek bukata domin kare lafiyarsu da gina jiki, tare da kare jiki daga wasu cuce-cuce masu kama jarirai da yara kananan.

Shayar da nonon uwa
Shayar da nonon uwa

Wata likita a sashen Kula da Lafiyar Jarirai da Yara Kanana a Hukumar WHO, Bernadette Daelmans, ta ce shayar da nonon uwa yana da amfani mai yawa ga lafiyar yara a gajere da kuma dogon lokaci. Ta ce, "Mu a nan Hukumar Kiwon lafiya ta Duniya da kuma Asusun Tallafawa Yara na Majalisar Dinkin Duniya, UNICEF, mun yi imanin cewa za a iya ceto rayukan yara miliyan daya da rabi daga cikin 'yan kasa da shekara biyar su miliyan takwas da dubu dari takwas dake mutuwa kowace shekara, idan har a watanni 6 na farko da haihuwarsu ba za a ba su komai ba sai nonon uwa, kuma za a ci gaba da shayar da su nonon uwar tare da wasu kayan abincin har na tsawon shekaru biyu."

Hukumar WHO ta ce rashin abinci mai gina jiki shi ne ke haddasa mutuwar sulusin yara kusan miliyan 9 'yan kasa da shekara 5 dake mutuwa kowace shekara.

Dr. Daelmans ta ce jarirai da yaran da suka sha nonon uwa, su na ganin moriyar wannan har zuwa lokacin da suka balaga, tana mai cewa "...shayar da nonon uwa tana da amfani domin tana rage hawan jini ga mutane idan sun balaga. Balagaggun da suka sha nonon uwa lokacin da suke jarirai ko yara, ba su cika ganin kitse mai yawa a jininsu ba. Ita ma uwa tana cin moriya saboda shayarwa tana rage mata kasadar kamuwa da cutar sankara ta mahaifa ko ta nono."

Shayar da nonon uwa
Shayar da nonon uwa

Hukumar WHO da Asusun UNICEF sun kirkiro da wasu matakai goma da cibiyoyin kula da lafiya da sibitoci zasu iya amfani da su domin tabbatar da nasarar shayar da yara nonon uwa. Alal ga misali, matakan sun kunshi taimakawa uwaye yadda zasu fara shayar da jariransu cikin minti 30 da haihuwa, tare da koya musu yadda zasu yi hakan.

Hukumar WHO ta ce a yanzu haka, asibitoci a kasashe fiye da 150 su na yin amfani da wadannan matakai guda 10.

Melinda Gates

BIDIYO: COVID-19 VOA Ta Yi Hira Da Melinda Gates Kan Dalilin Da Yasa Suke Taimakawa Afirka
please wait

No media source currently available

0:00 0:03:08 0:00
Karin bayani akan Bidiyo
XS
SM
MD
LG