Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Annobar Cutar Kwalara Tana Barazana Ga Dukkan Najeriya Yanzu


Kwayar Cutar Kwalara

Ma'aikatar lafiya ta Najeriya ta ce cutar ta bulla a jihohi akalla 11, ta kuma kashe mutane fiye da dari uku da hamsin ya zuwa yanzu.

Ma'aikatar kiwon lafiya ta Najeriya ta ce annobar cutar kwalara da ta bulla kwanakin baya, tana yin barazana ga dukkan kasar a yanzu.

Ma'aikatar ta fada a cikin wata sanarwa jiya laraba cewa annobar ta kashe mutane fiye da 350 a cikin 'yan watannin nan. Ta ce a yanzu, likitoci sun gano cutar a jihohi 11, kuma an samu mutane fiye da dubu 6 da 400 wadanda suka kamu da ita.

Jami'ai sun dora laifin bullar annobar a kan shan ruwan da ya gurbace da kuma rashin tsabta. Cutar kwalara tana haddasa mummunar gudawa da amai, abinda ek sa ruwan jikin mutum ya kare cikin dan kankanin lokaci. A saboda kwayar cutar tana girma ta fara illa a jikin mutum cikin dan kankanin lokaci, tana iya kisa idan har ba a yi maganinta da wuri ba.

Haka kuma a jiya larabar, ma'aikatar kiwon lafiya ta Najeriya ta ce cutar bakon dauro ta kashe mutane 83 a wannan shekarar, yayin da mutane fiye da dubu biyar suka kamu da ita. Ta ce tana shirin kara wayar da kan jama'a game da alamun cutar da kuma hanyoyin rigakafinta.

Wata kwayar cuta mai saurin yaduwa ita ce take haddasa bakon dauro. Kwayar cutar tana nakkasa garkuwar jikin mutum, amma ana iya rigakafinta cikin sauki. Alamun cutar sun hada da tari, da yoyon hanci, da zazzabi da kuma kuraje jajaye wadanda su na iya yaduwa zuwa dukkan jikin mutum.

XS
SM
MD
LG