Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Hukumar Kiwon Lafiya Ta Duniya Za Ta Fara Gwajin Maganin Rigakafin Cutar Cizon Sauro


Babbar Daraktar Hukumar Kiwon Lafiya ta Duniya, WHO, Margaret Chan
Babbar Daraktar Hukumar Kiwon Lafiya ta Duniya, WHO, Margaret Chan

Hukumar kiwon lafiya ta duniya wato WHO zata fara gwajin maganin rigakafin cutar zazzabin cizon sauro a wasu kasashen Afirka uku

Hukumar kiwon lafiya ta duniya wato, WHO a takaice ta zabi kasashen Ghana da Kenya da kuma Malawi sukasance kasashe na farko da za’a fara gwada maganin hana kamuwa da cutar Malariya na farko wanda za’a gwadashi shekara mai zuwa a kan kananan yara.

Maganin da za’ayi allurarsa wanda a kafi sani da suna RTSS ko kuma Mosquirix an kirkire shi ne a ma’aikatar kamfanin hada magunguna ta Birtaniya, GlaxoSmithKline.

Za’ayi wannan gwaji ne akan jarirai da kuma yan yara kanana yan watanni 15 zuwa 17.

Facebook Forum

XS
SM
MD
LG