Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Hukumar Kiwon Lafiya ta Duniya zata kira taron gaggawa akan kwayar Zika


Margaret Chan shugabar hukumar kiwon lafiya ta duniya

Kwayar zika dake sa a haifi jajrirai da nakasa daga cizon sauro ake samunta tana shiga jikin mata idan kuma sundauki ciki ta haddasa nakasa

Ranar Litinin mai zuwa ne ake kyautata zaton hukumar ta kiwon lafiya zata yi taron gaggawa saboda lalubo hanyar dakile yaduwar kwayar da cutar da take haddasawa.

Hukumar Kiwon Lafiya ta Duniya tace yadda kwayar ke yaduwa a duniya nada bada tsoro. Kawo yanzu kwayar ta kai kasashe 23 ko. Idan mace nada kwayar duk lokacin da ta dauki ciki, to jaririnta na iya samun nakasa kamar a haifeshi da karamin kai da kwakwalwar da bata da cikakken anfani.

Hukumar Kiwon Lafiya ta Duniya ko WHO ta yi gargadin cewa miliyoyin mutane a kasashen dake yankin tsakiya da yammacin Amurka ka iya kamuwa da cutar. Saidai a wadannan wuraren tuni mahukunta suke anfani da hanyoyin da aka sani da wadanda ba'a sani ba domin dakile yaduwar kwayar Zika.

Misali, a kasar Honduras hukumomi sun tashi haikan suna anfani da manyan motoci suna feshi koina domin dakile yaduwar kwayar.

Shugabar makarantar horas da likitoci ta kasar Honduras tace "sauro ne ke yada kwayar saboda haka dole ne mu zabura mu yaki sauro ta hanyar tsaftace rundunoninmu da bayan gidajenmu da duk abubuwan da muke tara ruwa ciki da ciki da kewayen muhallanmu. Yin hakan na bukatar kokarin mutane. Idan kuma muka kasa to akwai hadarin tsaftace muhallanmu.

Bugu da kari kasar Honduras ta shiga kamfen na fadakarwa da illimantar da jama'a musamman mata masu juna biyu. Likitoci sun ce kwayar ta haddasa haifuwar yara da kananan kawuna da kwakwalwa mai taikataccen aiki.

Idan har za'a shawo kan wannan cutar to wajibi ne jama'a su kula da tsafta kodayaushe, ba wai a yi yau ba gobe a koma gidan jiya.

A Amurka cibiyar dake hana yaduwar cututtuka ta gargadi mata masu juna biyu kada su yi balaguro zuwa kasashen da aka tabbatar kwayar ta bulla kamar kasar Brazil inda dubban mutane ne aka ce sun kamu da kwayar.

XS
SM
MD
LG