Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Hukumar Kiwon Lafiya Ta Duniya Zata Taimakawa Najeriya da Allurar Polio


Shugabar Hukumar Kiwon Lafiya ta Duniya ko WHO, Margaret Chan
Shugabar Hukumar Kiwon Lafiya ta Duniya ko WHO, Margaret Chan

An yi shekaru biyu cur ba'a samu cutar shan inna ba a Najeriya sai makonni biyu da suka shude aka ji labarin barkewar cutar a sansanin 'yan gudun hijira da rikicin Boko Haram ya daidaita a arewa maso gabashin kasaar.

Wannan sabon labarin sake bullar cutar a Najeriya ya zo ne bazata wa hukumomin kasar, ya kuma tada hankalin al'ummar kasar da na kasashen dake makwaftaka da ita.

To saidai matakan gaggawa da hukumomin Najeriya suka dauka sun farantawa hukumar kiwon lafiya ta duniya rai har ma shugabar hukumar ta kira ministan kiwon lafiya ta zanta dashi.

A firar da yayi da Muryar Amurka Dr. Nasiru Gwarzo, daraktan ma'aikatar kiwon lafiya ta Najeriya wanda yake kula da cututtuka ya bayyana gamsuwar ita shugabar hukumar kiwon lafiya ta duniya Dr. Margaret Chan da kuma alkawarin ba Najeriya gagarumin taimako.

A cikin allurar rigakafi kusan miliyan dari ukku da ake bukata hukumar zata bada miliyan dari biyu kafin karshen wannan shekarar.

Ga karin bayani.

please wait

No media source currently available

0:00 0:03:48 0:00

XS
SM
MD
LG