Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Hukumar Kiwon Lafiya Ta Duniya Ta Karbe Rawani Jakadanci Data Baiwa Robert Mugabe.


Shugaban hukumar kiwon lafiya ta Duniya Tedros Adhanom.
Shugaban hukumar kiwon lafiya ta Duniya Tedros Adhanom.

Shugaban hukumar wanda ya bada sanarwar nadin ranar Asabar, shine kuma ya bada sanarwar janye rawanin Lahadin nan.

Hukumar kiwon lafiya ta duniya WHO ta janye jakada na musamman data baiwa shugaban Zimbabwe Rober Mugabe.

Na saurari dukkan wadanda suka bayyana ra'ayoyinsu, da dalilai da suka bayar. Haka nan na tuntubi gwamnatin Zimbabwe, baki daya mu amince cea shawarar janye bashi wannan mukami shine yafi dacewa ga muradun wannan hukumar onji shugabanta Tedros Adhanom Ghebresusu.

Kungiyoyin rajin kare hakkin Bil'Adama da sauransu nr suka yi ca kan nadin na shugaba Robert Mugabe. Suna zargin cewa bai cancancin wannan mukamin ba, saboda take takensa sun saba manufofi da ala'dun hukumar.

Wata kungiya mai sa ido kan harkokin Majalisar Dinkin Duniya da ake kira UN Watch mai cibiya a Geneva, ta zargi shugaba Mugabe a zaman wanda ya ci zarafin masu rajin demokuradiyya, da ire irensu ya kuma tsiyata kasar da zata iya wadata Afirka baki daya da abinci.

Facebook Forum

XS
SM
MD
LG