Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Hukumar lafiya ta Duniya ta amince a ba masu lafiya maganin cutar kanjamau


Wata mata da yaro masu cutar kanjamau
Hukumar lafiya ta duniya ta goyi bayan ba wadanda suke gudun kamuwa da cutar kanjamau maganin rashin kaifin cutar. Hukumar ta kuma shawarci kasashe masu karfin arziki su kaddamar da tsarin gwada shirin domin a kara fahimtar amfanin shirin.

Hukumar ta bada wannan shawarar ne bayan masu sa ido kan ingancin magunguna na Amurka suka amince da maganin da rage kafin cutar kanjamau da ake kira Truvada, ga mutanen da basu dauke da cutar amma yana yiwuwa su yi jima’I da wadanda ke dauke da cutar kanjamau. Ana kiran wannan tsarin da turanci “pre-exposure prophylaxis”, ko PrEP a takaice.

Ana amfani da maganin Truvada ya kunchi sauran magungunan da ake amfani da su wajen rage kaifin cutar kanjamau a jinyar wadanda ke daukar da kwayar cutar HIV dake haddasa cutar kanjamau. Maganin da kudin amfani da shi ya kai dala dubu 14 a shekara a Amurka, shine magani rigakafin kamuwa da cutar na farko da aka amince da shi.

Hukumar lafiya ta duniya tana karfafa kasashen da suke sha’war amfani da tsarin rigakafi na PrEP su fara kaddamar da shirin wayarwa da ma’aikatan jinya kai dangane da amfanin shirin kafin aiwatar da shi. Hukumar ta kuma kafafa bada magungunan kanjamau ga wadanda suke fuskantar barazanar kamuwa da cutar.

Kawo yanzu sama da kasashe 112 da suka hada da kasashen da suka fi fama da cutar HIV kamar Indiya da Thailand da kuma Afrika ta Kudu, suna samun magunguna masu saukin kudi dake kama da maganin Truvada,da kudinshi mai wuce dala 8 ba a wata, Karkashin wani shiri na musamman na wadansu kamfanonin magani na kasar Indiya.
An gudanar da binciken na PrEP ne tare da tallafi daga gidau niyar Bill da Milinda Gates a yunkurin magance yada kwayar cutar kanjamau.

Melinda Gates

BIDIYO: COVID-19 VOA Ta Yi Hira Da Melinda Gates Kan Dalilin Da Yasa Suke Taimakawa Afirka
please wait

No media source currently available

0:00 0:03:08 0:00
Karin bayani akan Bidiyo
XS
SM
MD
LG