Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Hukumar Lafiya WHO Ta Yi Taron Neman Kawo Karshen Kwalara A Yankin Tafkin Chadi


Wani yaro dake fama da cutar Kwalara
Wani yaro dake fama da cutar Kwalara

Hukumar Lafiya ta Majalisar Dinkin Duniya WHO, ta shirya wa kasashen yankin Tafkin Chadi wani taron neman kawo karshen cutar Kwalara a yankin.

A taron masana sun tattauna kan yadda za a kawo karshen annobar Kwalara a kasashen. Daya daga cikin kwararrun da suka wakilci Najeriya a taron daraktan ma’aikatar lafiya Dakta Nasiru Sani Gwarzo, yace a kwai matakai da aka yanke tsakanin kasa da kasa wanda ake kira Cross Border.

Kasancewar a baya idan an sami wata annoba ta bullo akwai wasu matakai masu tsawo da mutane ke bi kafin daga karshe ta kai ga hukumar WHO, amma yanzu an yanke shawarar cewa a karfafa kwamitin ma’aikatan dake bakin iyaka domin tabbatar da ganin an dakile yaduwar cutar.

Duk da yake kusan duk shekara sai an sami bullar annobar Kwalara a yawancin kasashen. Tsaftace muhalli da abinci kadai ake bukata wajen kawar da annobar inji Nasiru Sani Gwarzo, yace kuma kusan duk fadin duniya babu inda annobar Kwalara tayi katutu irin kasashen Hudu na tafkin Chadi.

Domin karin bayani.

please wait

No media source currently available

0:00 0:02:12 0:00

XS
SM
MD
LG