Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Wasu NGO Sun Bukaci Hukumar EFCC Ta Kara Bayanin Ayyukanta A Shiyar Kano


EFCC
EFCC

Shiyar Kanon ta EFCC ta kunshi jihohin Kano, da Jigawa, da Katsina, da Kaduna, da Zamfara , da Sokoto da Kebbi

Barrister Aisha Tahir Habib babbar jami'ar dake kula da harkokin shari'a na hukumar EFCC a Kano tace manema labarai na kukan cewa hukmar bata basu labarai akan ayyukansu saboda haka suka fitar da wasu bayanai.

Barrister Aisha tace basa boye abubuwan da su keyi. Injita sun samu nasarori bisa kararrakin da suka shigar har 23 cikin watanni goma. Sun kwato dalar Amurka $600,022 da wasu kayayyaki da suka karba daga mutane da kuma wasu kudade a bankuna. Baicin hakan akwai kuma gidaje da wasu dukiyoyi.

Aisha tace basa cewa ga abubuwan da suka kwato daga hannun 'yan siyasa ko kuma wasu daban. Tace suna hada jimilla ne su bayar.

To saidai kungiyoyin fararen hula ko NGO suna cewa akwai bukatar ita hukumar EFCC ta yi karin bayani domin 'yan Najeriya su kara fahimtar abun da hukumar ke fadi.

Lauya Audu Bulama na cibiyar tabbatar da 'yancin 'yan kasa da zaman lafiya yace bayanan da EFCC tayi bata fito da abubuwan da ake son a sani ba. Yakamata hukumar ta bayyana su wanene ta kai kara kuma da wane laifi aka cajesu. Menene hukumcin da aka yi masu. Shin akwai biyan diya ko babu. Yace idan sun samu hukumci 23 cikin watanni 10 to guda nawa suka rasa. Misali idan an shigar da kararraki 70 aka samu 23 to akwai matsala.

EFCC tace ta karbi kudade a wurin wa aka karbi kudaden? Yaya suka yi da na daidaikun mutane? Yaya suka yi da na kamfanoni?

Shi kuwa kwamred Kabiru Saidu Dakata na wata kungiya cewa yayi ya kamata hukumar ta EFCCta kara kaimi domin wanke kanta daga zargin cewa duka ayyukansu sun karkata ne ga wasu rukunin mutane. Yace su har yanzu basu gamsu da yadda ake yaki da cin hanci da rashawa a kasar ba musamman idan aka yi la'akari da wasu zarge zarge dake yawo akan wasu manyan jami'an gwamnati tarayya.

Dakata ya bada misali da ministan sufuri Amechi wanda aka zarga da mikawa alkalai na goro. Akwai kuma Malam Abba Kyari shugaban ma'aikatan fadar shugaban kasa shi ma ana zargin ya karbi cin hanci na miliyoyin nera. Babacir Lawal David sakataren gwamnati ana zarginsa da jagoran wasu ayyuka na nera biliyan daya. Idan hukumar na son 'yan Najeriya su yadda da ita to ta hasakaka fitilarta kan mutanen.

Ga rahoton Mahmud Ibrahim Kwari da karin bayani.

please wait

No media source currently available

0:00 0:03:32 0:00

XS
SM
MD
LG