Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Hukumar NEMA Ta Kai Dauki Ga ‘Yan Gudun Hijira A Jihohin Adamawa Da Taraba


A daidai lokacin da jama'a a Najeriya ke ci gaba da kokawa game da matsalolin rayuwa, musamman abinci, hukumar kai agajin gaggawa NEMA ta kai dauki ga ‘yan gudun hijira wadanda tashe-tashen hankulan Boko Haram da kuma fadace-fadacen kabilanci ya shafa a jihohin Adamawa da Taraba.

Ya zuwa yanzu akwai ‘yan gudun hijira dubu uku da dari tara da talatin da shida (3,936) a sansanonin Malkohi, St. Theresa da kuma Fufore wadanda rikicin Boko Haram ya raba su da gidajen su a jihar Adamawa.

Hukumar ta NEMA, wadda ke kula da sansanonin ‘yan gudun hijira ta ce, za ta ci gaba da kai tallafin abinci ga ‘yan gudun hijirar a duk wata, a cewar jami’in hukumar NEMA Mallam Abubakar Sadik Nuhu, wanda shi ya jagoranci raba kayyakin abincin a sansanin ‘yan gudun hijira dake Fufore.

Daya daga cikin shugabanin ‘yan gudun hijira a sansanin na Fufore, Bakura Umar Mika ya ce, suna kira ga gwamnati da ta taimaka musu da wurin zama, da kuma jari.

Bayan kai tallafin ga sansanonin ‘yan gudun hijira da tashin hankalin Boko Haram ya shafe su, hukumar ta NEMA ta kai tallafi na musamman ga wasu da tashin hankalin kabilanci ya raba da gidajensu a yankin Guyuk, Lamurde da kuma jihar Taraba.

Mr. Midala Iliya Anuhu, jami’in hukumar ta NEMA mai kula da jihohin Adamawa da Taraba, ya bayyana irin tallafin da suka kai, kamar kayan abinci da dai sauransu.

Facebook Forum

XS
SM
MD
LG