Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

‘Yan Mata 7 Sun Mutu a Wani Shagon Gyaran Gashi a Jihar Neja


Hukumomi a jihar Neja a Nigeria sun kaddamar da bincike don gano dalilin mutuwar wasu ‘yan mata guda 7 da sanyin safiyar ranar juma’a 31 ga watan Yuli, a daidai lokacin da ake shirin idin Babbar Sallah.

Wannan al’amari dai ya faru ne a garin Rijau da ke jihar Neja, bayanai sun nuna cewa ‘yan matan su 6 sun je wani shago ne da ake gyran gashi domin yin kitson sallah amma daga bisani sai dai aka ga gawarwakinsu tare da mai gyaran gashin. Uku daga cikin 'yan matan daga iyali daya suka fito.

Shugaban karamar hukumar Rijau Honarabul Bello Bako, ya ce ya bada umurnin a yi wa yaran jana’iza kafin daga bisani a ci gaba da bincike, yayin da daya daga cikin iyayen yaran Alhaji Abdulrazak Rijau, ya ce iya abinda ya sani shi ne yaran sun tafi kitso, kawai sai dai aka kira shi aka fada masa abinda ya faru.

Rudunar ‘yan sandan jihar Neja ta tabbatar da aukuwar lamarin inda kakakin ‘yan sandan jihar ASP Wasiu Abiodun ya ce suna kan binciken lamarin.

Gwamnatin jihar Neja, a ta bakin sakatarenta Ahmed Ibrahim Matane, ta bayyana lamarin a matsayin "mai tayar da hankali" ta kuma jajanta wa iyalan mamatan.

Saurari karin bayani cikin sauti.

please wait

No media source currently available

0:00 0:02:39 0:00


Facebook Forum

XS
SM
MD
LG