Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Hukumar Hana Sha Da Fataucin Miyagun Kwayoyi Ta Yi Gagarumin Kamu


Hukumar hana sha da safarar muggan kwayoyi a Najeriya, NDLEA, ta bayyana kame kilo 455.215 na haramtattun kwayoyi a filin sauka da tashin jiragen sama Murtala Mohammed dake Lagos, wadanda adadin kudinsu yakai kusan Naira Bilyan 3 daga watan janairu zuwa Yunin bana.

A wata sanarwa da hukumar ta rabawa manema labarai a birnin Lagos, ta ce bugu da kari hukumar ta kwace zunzurutun kudi har dalar Amurka miliyan biyu da rabi, da kame wasu mutane saba'in da biyar wadanda suka hada da maza sittin da biyu da mata goma sha uku masu alaka da safarar muggan kwayoyi.

Hukumar ta kara da cewa ta cafke wani mai canjin kudaden ketare da kudi sama da dalar Amurka miliyan biyu da ya yi kokarin ficewa da su zuwa kasashen ketare wanda a yanzu haka an mika shi ga hukumar EFCC.

A cewar shugaban hukumar ta NDLEA, Alhaji Umaru Gyade, hukumar zata ci gaba da kama masu safarar muggan kwayoyi ganin irin illar da suke ma al'uma da tattalin arzikin kasa.

Shugaban hukumar ya kara da cewa a yanzu haka dai hukumar ta su ta samu hadin kan majalisar dinkin duniya na kudade da suka bada wadanda za'a koya wa ma'aikatan dabarun aiki iri iri domin kara inganta aikin su na binciken laifuffuka, da kuma gine gine wanda za'a sa wadanda suka kamu da masifar shaye shaye domin taimaka masu dawowa ciki haiyacin su da kuma daina wannan hali.

Irin nau'in kwayoyin da hukumar take yawan kamawa sun hada da tabar wiwi, da kwayoyin Ephedrine Methamphetamine, da hodar iblis ta Cocaine da Tramadol. kuma akasarin kwayoyin kamar yadda shugaban hukumar ya bayyana, ana shigo da su ne daga kasar Brazil, kana kuma ake neman safarar su zuwa kasar China.

Ga rahoton Babangida Jibrin.

Hukumar Hana Sha Da Fataucin Miyagun Kwayoyi Ta Yi Gagarumin Kamu - 2'44"
please wait

No media source currently available

0:00 0:02:44 0:00
Shiga Kai Tsaye

Shin PI Za Ta Fashe Kuwa Ko Yaudara Ce Kawai?

Karin bayani akan Bidiyo
XS
SM
MD
LG