Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Hukumar Tace Fina Finai Ta Jihar Kano Tayi Kashedi


Jarumin Fina-Finan Hausa, Ali Nuhu

Sannan kuma za ta kiyaye abubuwa guda uku

Hukumar tace fina finai da sauran ayyukan fasaha ta jihar Kano tace zata sanya kafar wando guda da masu wallafa takardu da hotunan batsa da sunan suna tallan magunguna da wasu kayayyakin amfani.

Shugaban hukumar Ismaila Na Abba Afakalla,ya ce baya da tace fina finai domin tabbatar da cewar sunyi daidai da addini da kyawawan aladun Hausawa, hukumar nada hurumin sa ido akan abubuwan da suka shafi aiyukan fasaha da wallafe wallafen kasidu da litattafe masu dauke da sakoni ga al’uma, da nufin ganin cewa babu lafuza ko hotunan batsa a cikin su.

Ya ce hukumar ba wai akan fim kawai ta tsaya ba an dora ta ne akan turaku guda hudu ta kare addini, ta kare kyawawan al’adun mu sannan ta kare zamantakewa da take tsakanin mu kada wanna ya zagi wanna addini kada mai wannan addini ya zagi wanna, kada kuma mai wanna kabila ya zagi wance kabila ko ta hanyar waka ko ta rubuce rubuce sannan kuma ta habaka sana’a.

Sannan kuma za ta kiyaye abubuwa guda uku ta kiyaye abunda mutane zasu gani ya shafi hoto mai motsi ko mara motsi sannan ta kiyaye abunda mutane zasu furta.

Malam Ismaila Na Abba, ya ce daga yanzu hukumar bazata saurarawa duk wanda ta kama yana da hannu wajen rusa tarbiyar jama’a, masamman kananan yara ba.

please wait

No media source currently available

0:00 0:03:30 0:00

Laftanar Janar Farouk Yahaya

Makasan Sheikh Goni Aisami Sun Bata Sunan Sojin Najeriya – Laftanar Janar Farouk Yahaya
please wait

No media source currently available

0:00 0:02:11 0:00
Karin bayani akan Bidiyo

Shin da gaske NNPP ba ta yi wa Shekarau adalci ba?

Karin bayani akan Bidiyo
XS
SM
MD
LG