Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Hukumar Wanzar Da Zaman Lafiya Ta Jihar Kaduna Ta Ce Ta Himmantu Ga Ganin An Yi Zaben 2023 Cikin Natsuwa

Hukumar Wanzar Da Zaman Lafiya Ta Jihar Kaduna Ta Ce Ita Zaben 2023 Cikin Natsuwa Ta Sa A Gaba
Hukumar Wanzar Da Zaman Lafiya Ta Jihar Kaduna Ta Ce Ita Zaben 2023 Cikin Natsuwa Ta Sa A Gaba

Hukumar wanzar da zaman lafiya ta Jihar Kaduna wato Peace Commission ta ce duk da kokarin da mahukunta ke yi game da matsalar tsaro, hare-haren 'yan-bindiga da matsalolin tsaro sun ta'azzara a wasu sassan Jihar cikin wannan shekarar.

KADUNA, NIGERIA - Hukumar wanzar da zaman lafiyar, wadda ta kira wani taron masu ruwa da tsaki, ta ce ta na sane da yankunan da ke fama da matsalolin tsaro a sassan Jihar Kaduna amma kuma ta na daukar matakan magance su.

Hukumar Wanzar Da Zaman Lafiya Ta Jihar Kaduna Ta Ce Zaben 2023 Cikin Natsuwa Ta Sa A Gaba
Hukumar Wanzar Da Zaman Lafiya Ta Jihar Kaduna Ta Ce Zaben 2023 Cikin Natsuwa Ta Sa A Gaba

Shugaban hukumar, Dr. Saleh Momale shi ya yi wa manema labarai bayani game da wannan taro. Momale ya ce manyan ayyukan da ke gaban hukumar sune zaben shekarar 2023 da kuma kidaya; saboda akwai bukatar zaman lafiya don gudanar da wadannan ayyuka biyu.

Malam Suleiman Abdul'Aziz wakilin masu bukata ta musamman a hukumar wanzar da zaman lafiyan ta Jihar Kaduna, ya ce hukumar za ta kira dukkan 'yan takara don su sanya hannu kan yarjejeniyar zabe cikin lumana a fadin Jihar baki daya.

Hukumar Wanzar Da Zaman Lafiya Ta Jihar Kaduna Ta Ce Zaben 2023 Cikin Natsuwa Ta Sa A Gaba
Hukumar Wanzar Da Zaman Lafiya Ta Jihar Kaduna Ta Ce Zaben 2023 Cikin Natsuwa Ta Sa A Gaba

Cikin kwanakin nan dai gwamnatin Kaduna ta ce jami'an tsaro na nasara a kan 'yan-bindigan da ke daji har ma ta ceto wasu mutane.

Kwamishinan tsaro da harkokin cikin gida na Jihar Kaduna, Malam Samuel Aruwan ya ce yanzu ayyuka na masamman jami'an tsaro ke yi a dazuzzuka kuma su na samun nasarori.

Hare-haren 'yan-bindiga har sun ma tashi garuruwa da dama a kananan hukumomin Birnin Gwari, Igabi, Chukun, Zangon Kataf da Giwa, sai dai ayyukan jami'an tsaro na baya-bayan nan sun soma samar da natsuwa a zukatan wasu al'ummar wadannan yankunan.

Saurari cikakken rahoton daga Isah Lawal Ikara:

Hukumar Wanzar Da Zaman Lafiya Ta Jihar Kaduna Ta Ce Zaben 2023 Cikin Natsuwa Ta Sa A Gaba.mp3
please wait

No media source currently available

0:00 0:03:24 0:00

XS
SM
MD
LG