Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Hukumar 'Yansandan Jihar Gombe Ta Kwance Bamabamai 12


Gwamnan jihar Gombe Ibrahim Dankwambo
Gwamnan jihar Gombe Ibrahim Dankwambo

Sanadiyar labarin asiri da jami'an tsaro suka samu hukumar 'yansandan jihar Gombe ta samu nasarar kwance wasu bamabamai goma sha biyu da aka dana cikin wata mota kusa da makaranta.

Cikin wata mota da aka ajiye kusa da wata makarantar sakandaren gwamnati, hukumar 'yansandan jihar Gombe ta samu ta kwance bamabamai har goma sha biyu.

Makarantar tana kusa da tashar motar Dukku dake cikin garin Gombe. Kakakin hukumar 'yansandan Mr. Faja Attajiri yace sun samu nasarar kwance bamabaman ne bayan sun samu rahoto daga jama'ar gari.

Yansandan da suka kware akan harkar bamabamai suka je inda aka ajiye motar suka kwance bamabaman. Idan da bamabaman sun tashi to da sun yi mummunan barna na rayuka da dukiyoyi. An cire bamabamna kuma an gayawa jama'a kada su tada hankalinsu.

Dama an riga an fadakar da mutane idan sun ga abun da basu yadda dashi ba su gayawa hukuma. Abun da ya faru ke nan. Da mutane suka ga motar sai suka gayawa 'yansanda su kuma suka dauki mataki ba tare da bata lokaci ba.

Kawo yanzu babu wanda aka kama amma 'yansanda suna cigaba da bincike.

Ga rahoton Abdulwahab Muhammed

please wait

No media source currently available

0:00 0:02:25 0:00
Shiga Kai Tsaye

XS
SM
MD
LG