Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

APC Ta Lashe Zaben Gwamnan Jahar Osun-INEC


Shugaban hukumar zabe ta Najeriya Prof Mahmoud Yakubu.
Shugaban hukumar zabe ta Najeriya Prof Mahmoud Yakubu.

Hukumar zaben Najeriya mai zaman kanta ta ayyana Gboyega Oyetola na jam'iyyar APC a zaman wanda ya lashe zaben fidda gwani na gwamnan jihar Osun da ta gudanar ranar Alhamis.

Kamar yadda wasu kafofin yada labaran kasar suka bayyana, Jami'in zaben Parfessa Joseph Fuwape, ya ayyana dan takarar APC Oyetola, a zaman wanda ya lashe zaben .Ya sami kuri'u dubu 255, da 505, yayinda dan takarar jam'iyyar PDP Senata Adeleke, ya sami kuri'u dubu 255,023,

An sake gudanar da zaben ne a mazabu bakwai, wadanda hukumar zaben ta soke zaben su a zaben da aka gudanar ranar Asabar data wuce.

A zaben da aka gudanar ranar Asabar, dan takarar jam'iyyar PDP Ademola Adeleke, shine ya lashe zaben da kuri'u dubu 254,698, yayinda dan takarar APC ya sami kuri'u dubu 254,345.

Dan takarar na PDP, senata Adeleke, da jam'iyyar PDP, da kuma gamayyar jam'iyun siyasa sun yi tur da sakamakon zaben.

Zamu kawo muku karin bayani da zarar mun sami wani labari.

Facebook Forum

XS
SM
MD
LG