Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Hukumar Zabe Ta Najeriya Ta Yiwa Jam'iyyar APC Rijista


Almar jam'iyyar APC sabuwar jam'iyyar da ta sami rijista.

Babbar jam'iyyar hamayya a Najeriya APC ta sami amincewar hukumar zabe watau INEC.

Hadakar jam'iyun hamayya ACN da CPC da ANPP, gamayyar da ta haifar da jam'iyyar APC ta sami rijista.

Babban sakataren hukumar zabe ta Najeriya Abdullahi Kaugama ne ya tabbatar da haka cikin wata sanarwa da hukumar ta bayar, kamar yadda wakilanmu daga Abuja suka tabbatar.

Shi ma da yake magana akai daya daga cikin jiga-jigan jam'iyyar ACN, kuma tsohon gwamnan jihar Legas Alhaji Ahmed Bola Tinubu, yace yau ranar murna ce ga dokacin 'yan Najeriya. Saboda zasu sami zabi daga jam'iyyar PDP mai mulkin kasar ahalin yanzu.

Babban jami'in harkar mulki na tsohon gwamnan, kuma tsohon shugaban Sashen Hausa na Muriyar Amurka, Mallam Sunday Dare, yace wannan babban abun tarihi ne.

Ga kadan daga cikin abunda wakilin Sashen Hausa Nasiru Adamu El-Hikaya yake fadi kan rijistar, da kuma Sunday Dare, babban jami'in harkar mulki na gwamna Tinubu, kuma tsohon shugaban Sashen Hausa na Nuriyar Amurka.

please wait

No media source currently available

0:00 0:04:34 0:00
Shiga Kai Tsaye
XS
SM
MD
LG