Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Jam’iyyar PDP Ta Dakatar Da Ameachi


Hira da Shugaban Jam'iyyar PDP na Nigeria kan tsarin Karba-Karba

Jam’iyyar dake mulkin Najeriya ta dakatar da Rotimi Ameachi, Gwamnan jihar Ribas daga jam’iyyar yau Litinin bayan da ta ce ya karya wasu dokokin kundun tsarin mulkinta.

Wasu kusoshin jam’iyyar ne suka bayanna wa wakilin Amurka Umar Farouk Musa wannan labari.

A karshen makon da ya wuce ne, Gwamna Ameachi yayi takarar neman shugabancin kungiyar Gwamnonin Najeriya inda ya yi nasara akan Gwamnan Jihar Filato, Jonah Jang. Rahotanni sun nuna cewa Shugaba Goodluck Jonathan dan jam’iyyar ta PDP ya goyi bayan Gwamna Jonah Jang ne, kuma faduwar Mr. Jang bai yi wa shugaban dadi ba.

Dama a baya-bayanne ne, aka fara ganin alamun rashin jituwa tsakanin Gwamnatin kasa da Gwamna Ameachi, inda har aka hana jirgin Gwamnan tashi, aka janye jami’an tsaron dake kare magoya bayanshi, kuma aka kori wasu shuwagabannin PDP wadanda ake tunanin magoya bayan Ameachin ne, daga jam’iyyar.

Kafin fitowar sanarwar dakatar da shi, Gwamna Ameachi ya tsaye akan bakansa cewa shine zababben shugaban kungiyar gwamnoni ta Najeriya.

Wakilin Muryar Amurka a babban birnin Abuja ya rawaito cewa sabuwar jam’iyyar APC na sha’awar jawo Gwamna Ameachi domin ya shiga jam’iyyar.

please wait

No media source currently available

0:00 0:05:25 0:00
Shiga Kai Tsaye

Shin PI Za Ta Fashe Kuwa Ko Yaudara Ce Kawai?

Karin bayani akan Bidiyo
XS
SM
MD
LG