A kokarin da take yi na gudanar da ingantacen zabe hukumar zabe, INEC ta fara ilimantar da jama'a akan yadda ake kada kuri'a ta yadda ba zata lalace ba.
Hukumar zaben tana anfani da gidajen rediyo ne da talibijan domin fadakar da kawunan jama'a kafin zaben shekarar 2019..
Shugaban hukumar zaben, INEC, Farfasa Mahmud Yakubu ta bakin wanda ya wakilceshi Prince Adedeji Showobi ya bayyanawa jama'a a wajen wayar da kawunan masu zabe a Ibadan babban birnin jihar Oyo.
Yana mai cewa kwamitin yada labarai da ilimantar da masu zabe na hukumar ya kuduri aniyar hada kawunan duk jihohi da masu ruwa da tsaki a harkokin zabe a ilimantar dasu tare da tattaunawa da zummar aiwatar da manufofi daya tare.
An kira mai kada kuri'a ya fahimci yadda ake zabe domin kuri'arsa ta yi tasiri. Farfasa Yakubu yace duk da matsin tattalin arziki da kasar ke fama dashi ya kamata a ilimantar da masu zabe domin su bada tasu gudummawar idan lokaci ya yi..
Ga rahoton Hassan Umar Tambuwal da karin bayani.
Facebook Forum